A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, babban daraktan makarantun addini na Hauza, ya aike da saƙon ta'aziyya sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin manyan marja'an taƙalid na ƙasar Iraki, Ayatullah Al-Uzma Al-Fayyadh. Ga abinda saƙon yake cewa:
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un
Shugabanmu Imam Sadiƙ (AS) ya ce: “Idan masani na addini (Alim) ya rasu, to an kafa wata ɓaraka a cikin Musulunci wacce babu abin da zai iya toshe ta har zuwa Ranar Kiyama.”
A farkon babban bikin Eidullah al-Akbar, wato Eid al-Ghadir, kuma a cikin kwanakin cikar addini da kammala ni'ima, labarin rasuwar babban marja'i, Hazrat Ayatullah Al-Uzma Hajji Sheikh Muhammad Ishaƙ Al-Fayyadh ya sanya mu cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin zuciya.
Shi dai wannan babban malami, yana ɗaya daga cikin manyan daliban da suka koya a karkashin inuwar marigayi Ayatullah Al-Uzma al-Khu'i (Q). Kuma a tsawon rayuwarsa mai albarka da ciyar da gaba, bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen daukaka kalmar Allah da yada ingantattun ilimomi na Ahlul-Bait (AS). Ya bar manyan ayyuka da rubuce-rubuce na ilimi da fannin fiƙhu masu daraja waɗanda duka sun zama babbar taska ga makarantun addini na Hauza.
Sabbin abubuwan da ya kawo na ilimi da fikihu tare da hidimomin addini da na yada sakon Musulunci da wannan babban marja'i ya yi, musamman ma rawarsa da ba za a taɓa mantawa da ita ba wajen farfaɗo da tattakin Arba'in, da ayyukan tallafawa al'umma da na al'adu ga ƙasashe da musamman mutanen kasashen Iraki da Afganistan, sun mayar da shi wani babban jigo da ya fice a fagen ilimi.
Ina mika ta'aziyya ta musamman game da rashin wannan malami na Ubangiji ga gaban amintaccen wannan zamani Imam al-Mahdi (ATFS), da manyan marja'ai (Damat Barakatuhum), musamman ma babban marja'in birnin Najaf Hazrat Ayatullah Al-Uzma Al-Sistani (Damallahu Zillahush Sharif), da babban jagoran juyin juya halin Musulunci (Dama Izzuhu wa Zilluhu), da makarantun Hauza na Najaf, Qom da Afganistan, da dukkan makarantun addini gaba daya, da iyalan mamacin, 'ya'yansa masu daraja, ɗalibansa da masoyansa, sannan musamman ga al'umma da gwamnatocin ƙasashe biyu abokai da muke ƙauna, wato Iraki da Afganistan.
Muna rokon Ubangiji Madaukakin Sarki ya jaddada rahama da yardarsa ga wannan babban marja'i, sannan ya ba wa dangi da na kusa da shi hakuri da lada mai yawa. Ya yi rayuwa cikin farin ciki da daukaka, kuma ya wanzu cikin farin ciki da ɗaukaka.
Alireza A'arafi
Shugaban Makarantun Hauza
Ra'ayinka